1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Matsayar raba iko ta haifar da fata

Mahmud Yaya Azare MAB
July 17, 2019

Jagororin mulkin sojin Sudan da masu fafutulkar neman suyi sun rattaba hannu kan yarjejeniyar raba madafun iko tsakaninsu bayan makonni biyu na jan kafa, lamarin da ya haifar da martani daga bangarori dabam dabam.

https://p.dw.com/p/3MCoI
Sudan Khartoum | Mohamed Hamdan Dagalo und Protestführer unterschreiben Abkommen
Hoto: Getty Images/AFP/H. El-Tabei

Bayan kwashe dare ana tattaunawa a birnin Khartoum na kasar ta Sudan, wakilan majalisar sojin wucin gadi na kasar da masu fafutuka da masu shiga tsakani na Tarayyar Afirka da kasar Habasha sun sa hannu kan yarjejeniyar da za ta share fagen rabon iko a kasar. Mataimakin shugaban kasar ta Sudan Mahammad Hamdan Doglo Humaidty ya siffantata da wacce ba za a manta da ita a tarihi ba, inda ya ce: “Ina albishir ga al'ummar Sudan kan sanya hannu da aka yi kan wannan yarjejeniyar ta siyasa. Wannan lamari ne na tarihi ga al'ummar Sudan.”

Mai shiga tsakani na Tarayyar Afirka Muhammad Hassan Labbad ya siffanta yarjejeniyar da bude sabon shafin zaman lafiya da hada gwiwa don gina kansa da cin moriyar arzikinta: Ya ce “Wannan wani mataki ne mai mahimmanci da kasar Sudan ta shiga, na dinke barakar da ke tsakanin al'umominta da tafiya tare don shiga wani sabon zamani.”

Sudan Khartoum | Friedensgespräche
Sojoji za su ci gaba da fada a ji har lokacin zabe a SudanHoto: picture-alliance/AA/M. Hjaj

  Shi kuwa wakilin kasar Habasha Mahmud Dareed wanda ya fashe da kuka don murnar wannan nasarar shiga tsakanin a kan sulhun da suka yi, fata ya yi ga kasashen duniya su ba wa al'ummar Sudan hadin kai don ketare wannan siradin. Ya ce ”Wannan al'ummar ta Sudan mai halin kwarai bai cancanta duniya ta barta haka a daidaice kara zube ba.Ya zama wajibi kasashen duniya su ga karshen yaki da tashe-tashen hankula da neman ballewa. Dole muyi tsayuwar daka don ganin an tsame Sudan daga kangin talauci da takunkumin da aka kakaba mata.”

Wannan yarjejeniyar dai ita ce matakin farko na rabon muki a kasar, yadda a yanzu haka ake ci gaba da tattauna batun kundin tsarin mulki na wucin gadi wanda shi ma za'a rattaba hannu kan amincewa da shi ranar Jumma'a. Ana sa rai wannan yarjejeniya za ta kawo karshen tashin hankalin da kasar ta fuskanta a baya-bayan nan, kuma za a kafa gwamnati hadin gwiwa ta shekara uku inda kuma daga karshe za a gudanar da zabe

Umar Eldugairi mai magana da yawun daya daga cikin manyan kungiyoyin farar hula ya nuna dari-darinsa da yarjejeniyar, inda ya ce:

"Sa hannu kan wannan yarjejeniyar tamkar tilasta wa bangarori biyun ne amincewa da kundin da ke tafe. Amma mu tsoronmu anan shi ne, kar sai magana ta yi nisa a komo ga irin halin kwan-gaba kwan-bayan da akai ta yi a baya”  

Sudan | Demonstration in Khartoum
Ra'ayoyin masu fafutuka sun bambanta kan yarjejeniyar raba iko a SudanHoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Ita kuwa Rasha Ewad,wata mai fafutuka, tsoranta ita ce kasashen ketaren dake katsalandam kan lamuran Sudan ne: Ta ce:“Matsalar da wannan yarjejeniyar za ta iya fuskanta itace, akwai bangarori da dama daga waje da ke fakon yi mata dukan kwaf daya, wadanda ba sa kaunar ganin dimukaradiyya ta kafu a Sudan.”