Hadarin jirgi ya kashe mutane a Sudan
January 3, 2020Talla
Rahotanni sun nunar da cewa ma'aikatan jirgin su bakwai sun mutu, kana wasu alkalai uku da kuma fararen hula takwas ciki har da kananan yara da wani jami'in hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da iyalansa na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu yayin hadarin.
Ba a tabbatar da musabbabin faduwar jirgin nan take ba, amma yankin da jirgin ya yi hadarin na fama da rikicin kabilanci. Sama da mutane 40 sun mutu wasu da dama sun jikkata a wani artabu tsakanin kabilu da ba sa jituwa da juna a yankin a baya-bayan nan.