Sudan: Soji sun tarwatsa masu zanga-zanga
February 7, 2022Talla
Zanga-zangar ta yau dai ta ci karo ne da turjiyar jami'an tsaro inda suka y amfani da karfi wajen tarwatsa su gami da watsa musu hayaki mai sa hawaye a lokacin da suka tunkari fadar gwamnati da ke birnin Khartoum.
Al'umma a kasar dai na ci gaba da nuna fushinsu tun bayan hambarar da mulkin farar hula da janar Abdel Fattah al-Burhan ya jagoranta a watan Oktoban shekarar bara.
Kawunan 'yan kasar ta Sudan na a rarabe, a yayin da wasu ke kin amincewa da matakin sojojin, a karshen makon da ya gabata daruruwan masu goyon bayan sojojin sun gudanar da ta su zanga-zangar.