Gwamnatin hadaka tsakanin soji da farar hula a Sudan
April 29, 2019Bayan makwanni uku ana kai ruwa rana, daga karshe majalisar sojin wucin gadi kasar ta Sudan ta mika wuya bori ya hau ga bukatun masu zanga-zangar neman a kafa hukumar wucin gadi karkashin jagorancin farar hula, kamar yadda Izzul Arab, daya daga cikin wakilan masu fafutuka da aka yi zama karo na biyu da shi da majalisar wucin gadin sojin ya fadaw a gidan TV Aljazeerah.
"Wakilan masu fafutuka a zaman tattaunawar sun gabatar da shirin kafa gwamnatin gamin gambizar da sojin suka yi na'am da ita, wacce za ta kunshi jami'ai 15, bakwai sojoji, takwas fararen hular da za a zabosu daga bangarori mabambanta tare da yin la'akari da samun wakilcin matasa da mata a cikinta."
Tuni dai jagororin fafutukar neman sauyin a Sudan suka janye gudanar da zanga-zangar matsin lambar da aka shirya gudanar da ita a wannan Litinin, don nuna kyakkyawar aniya ga matakin da sojojin suka dauka, ko da yake har yanzu wadanda ke ci gaba da yin zaman dirshan da ke cewa suna nan kan bakarsu, na ci gaba da yin taka-tsantsan da wannan jawabi.
"Irin wannan shigo shigo ba zurfin mun jima da gane shi. Fada ne ba cikawa ba. Kullum sai su turo wani matashi ya fada wa duniya cewa, komai ya daidaita, washe gari kuma, sai ku ga ashe duk abin maganar fatar baki ce."
Hakan dai na wakana ne a daidai lokacin da kiraye-kirayen a hukunta tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir da kotun duniya ke nema ruwa a jallo ke karuwa. Shi dai tsohon shuganan da ke tsare a gidan yarin Kobra, an ruwaito cewa yana ta rusa kukan takaicin wulakancin da ya ce ana yi masa.
"Amincewar da sojoji suka yi na kafa gwamnatin gamin gambiza da fararen hula abin a yaba ne. Yanzu abin da ya rage musu shi ne daukar matakan hukunta al-Bashir da mukarrabansa, wadanda suka yi ta gasa wa 'yan Sudan aya a hannu tsawan shekaru 30 din da suka gabata."
Da ma dai tun kafin hakan, an jiyo mataimakin shugaban majalisar sojin, Janar Muhammad Hamdan Doglo, wanda shi ya jagoranci rundunar da ta hambarar da al-Bashir din yana zarginsa da mayar da rayukan 'yan Sudan ba a bakin komai ba don kare mulkinsa.
"Mun zo mun samu hambararen shugaba al-Bashir a lokacin da zanga-zanga ta yi kamari muka ce masa ranka ya dade to ya za a yi? Sai ya ce mana, kun san mu mabiya Mazhabar Malikiyya ne, wacce ta ba da fatarwar cewa, ka kashe daya bisa ukun 'yan kasa don mulki ya zauna lafiya, kai masu tsanani ma cewa suke, ko da rabin 'yan kasar ne ka kashe."
An dai zura ido a ga ko wannan sabon matakin zai kai go kwantar da hankalin 'yan kasar ta Sudan.