Sojoji sun kifar da gwamnatin al-Bashir
April 11, 2019Talla
Ministan tsaro a Sudan ya yi kira na a kama Shugaba Omar al-Bashir da ma kawar da gwamnatinsa bayan watanni da aka dauka a kasar ana zanga-zangar adawa da gwamantinsa ta tsawon shekaru 30. Dubban al'ummar kasar sun kwarara a tituna don ganin yadda za ta kaya bayan da aka shiga tattaunawa tsakanin sojoji da bangaren gwamnatin ta al-Bashir.