Sojojin Sudan za su shirya zabe a watanni tara
June 4, 2019Shugaban hukumar mulkin sojan kasar ta Sudan Abdel Fattah al-Burhane ne ya sanar da hakan a cikin wata sanrwa da ya fitar a safiyar wannan Talata a gidan talabijin na gwamnatin kasar inda ya ce za a shirya zabukan a bisa sa idon kasashen duniya.
Wannan mataki na sojojin kasar ta Sudan na zuwa ne kwana daya bayan da jami'an tsaron kasar suka yi amfani da karfin tuwo wajen murkushe zaman dirshen na masu zanga-zangar neman sauyi a gaban hedikwatar rundunar sojin kasar da ke a birnin Khartoum inda mutane sama da 30 suka halaka wasu daruruwa suka jikkata.
Sai dai hukumar mulkin sojan kasar ta musanta tarwatsa masu zaman dirshen din tare da yin alkawarin gudanar da bincike a kan abin da ya faru. Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da taro a a sirce a wannan Talata domin tattaunawa halin da ake ciki a kasar ta Sudan.