1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudin Sudan na fuskantar karyewar daraja

Zulaiha Abubakar
August 25, 2019

Sabon firaministan Sudan ya bukaci agajin kudin da yawansu ya kai dala biliyan takwas daga kasashen ketare a shekaru biyu masu zuwa don farfado ta tattalin arzikin kasar.

https://p.dw.com/p/3OSGS
Sudan Neuer Premierminister Abdalla Hamdok
Hoto: Reuters/M. Nureldin Abdallah

Firaminista Abdallah Hamdok wanda ya karbi rantsuwar aiki a makon da ya gabata biyo bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir ya bukaci karin wasu kudaden har dala biliyan biyu nan da watannin uku masu zuwa domin kare darajar kudin kasar daga barazanar karyewar.

A wata tattaunawarsa da manema labarai ba bayyana cewar tuni ya fara tuntubar asusun bayar da lamuni na duniya da kuma bankin duniya don sake yin duba a tarin bashin da ake bin kasar ta Sudan. Ya kuma kara da bayyana yadda ya bukaci kasar Amirka ta janye sunan kasar daga jadawalin kasashen da ke daukar nauyin ayyukan ta'addanci.