1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta bukaci tallafin kasashen duniya

Ahmed Salisu
April 14, 2019

Sabuwar gwamnatin rikon kwaryar Sudan ta bukaci agajin kasashen duniya wajen gudanar da aiyyukanta ciki kuwa har da kaiwa ga girka gwamnatin demokradiyya nan da shekaru 2 kamar yadda shugabanta ya yi alkawari.

https://p.dw.com/p/3GlE1
Sudan Militärrat Abdel Fattah al Burhan
Hoto: picture-alliance/AA

Wannan kira na gwamnatin Sudan din na zuwa ne daidai lokacin da 'yan kasar ke cigaba da nuna rashin amincewarsu da kasancewar soja a matsayin wanda zai jagoranci kasar kafin mika mulki ga zababbiyar gwamnati. Tuni dai kasashen duniya ciki har da Jamus suka yi kira ga 'yan Sudan da su yi kokari wajen ganin halin da ake ciki bai dagula lamura a kasar ba yayin da a share guda Saudiyya da Ingila suka yi alkawari na agazawa Sudan din ta fuskoki da dama ciki kuwa har bada tallafi ga al'ummar kasar da ke ciki yanayi na bukata.