Shagulgulan bayan cimma yarjejeniyar kafa gwamnati
July 5, 2019Mohammed el-Hassan Labat, shi ne wakilin Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU da ke shiga tsakani, ya ce bangarorin biyu sun amince da raba manyan mukamai a tsakaninsu inda kowanne bangare zai sami kujeru biyar biyar. Kungiyar AU da gwamnatin kasar Habasha sun taka muhinmiyar rawa wajen ganin an cimma matsaya bayan sabanin da aka samu biyo bayan wani hari kan masu zanga-zanga da ya mayar da hannun agogo baya a kulla yarjejeniyar samar da gwamnatin hadaka.
Mutum fiye da dari biyu da hamsin ne suka halaka tun bayan hambarar da gwamnatin Oumar al-Bashir a Disambar bara. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi hukumomin kasar ta Sudan da su kaddamar da bincike don gano wadanda keda hannu a amfani da karfi kan masu zanga-zanga.