Sudan ta Kudu: Amfani da yara wajen yaki
August 19, 2016Talla
Wata sanarwa da UNICEF din ta fidda ta nuna cewar wani babban jami'in gwamnati ne ke wannan aiki bisa umarnin shugaban kasar Salva Kiir. Rahoton har wa ya yau ya ce an yi amfani da tursasawa wajen daukar wadannan yara da ma basu horo, inda ya kara da cewar wasunsu ma ba su gaza shekaru 12 na haihuwa ba. Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance yawan yaran da aka dauka ba yayin da wata majiya ta rundunar sojin kasar ta Sudan ta Kudu ta ce zance ma sam ba haka ya ke ba domin wanda ke samun horon na soji matasa ne kuma suna yin haka ne don radin kansu.