Sudan ta Kudu: An gano gawar dan jarid
November 2, 2016
Kungiyar ta ce an gano gawar ce a ranar Litinin da ta gabata a cikin wata gona kusa da wani kauye mai suna Kerepi na kusa da kan iyaka da kasar Uganda inda mahaifansa ke da zama.
A ranar hudu ga watan Yulin da ya gabata ne dai wasu mutane masu sanye da kayan soja suka je gidan dan jaridar mai zaman kansa inda suka yi awon gaba da shi da wani kanensa mai suna Andruga. Kuma wasu shaidun ganin da ido sun shaida cewa mutanen da suka sace Isaac Vuni din na sanye da kayan dakaran Shugaba Salva Kiir.
Kungiyar ta RSF ta ce an kashe dan jaridar ne jim kadan bayan sace shi, sai dai kuma har yanzu babu duriyar kanan nasa da aka sace su tare. Ta kuma yi kira ga mahukuntan kasar da Sudan ta Kudu da su gaggauta bude bincike domin gano wanda ke da alhakin kisan dan jaridar dama gurfanar da shi a gaban kuliya domin hukunta shi.