Sudan ta Kudu da kokarin magance Boko Haram a Najeriya
August 22, 2015A sharhin da ta yi kan kasar Sudan ta Kudu jaridar Neue Zürcher Zeitung ta fara ne da cewa fatan samun zaman lafiya a Sudan ta Kudu ya ruguje a daidai lokacin da kasar ke kara tsunduma cikin talauci da yake-yake.
Jaridar ta ce a cikin bukukuwa da farin ciki a shekarar 2011 Sudan ta Kudu ta yi bikin 'yancin kai daga Sudan, bayan shekaru gommai na yaki, amma ba da jimawa ba murna ta koma ciki. A tsakiyar 2013 shugaba Salva Kiir ya kori mataimakinsa Riek Machar, a karshen wannan shekara an zargi Machar da yunkurin juyin mulki, tun daga wannan lokaci dai kasar ba ta ga zaman lafiya ba, duk kuwa da jerin tarukan sulhu da kuma yarjeniyoyin zaman lafiya da bangarorin da ke rikicin da juna suka sanya wa hannu.
Rashin tabbas a Sudan ta Kudu
Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi tsokaci a kan rikicin na Sudan ta Kudu tana mai cewa an sanya hannu kan yarjeniyoyi bakwai na neman zaman lafiya a kasar, amma an karya su. Saboda haka ba abin mamaki ba ne da a ranar Litinin da ta gabata aka fuskanci wani koma-baya dangane da sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya. Ko da yake jagoran 'yan tawaye Riek Machar ya albarkaci yarjejeniyar, amma Shugaba Salva Kiir bai rattaba hannu ba. Ya nuna bukatar a ba shi karin lokaci na kwanaki 15 na abin da ya kira "tuntuba". Sai dai tun farko ya yi zargin an matsa lamba, wanda ya ce ba abin karbuwa ba ne.
Kokarin kawo karshen Boko Haram
Shugaban Najeriya ya alkawarta samun nasara inji jaridar Der Tagesspiegel inda ta rawaito cewa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar ya ba wa sojojin kasar wa'adin watanni uku da su murkushe kungiyar Boko Haram, sai dai fa a cewar jaridar har yanzu 'yan ta'addan na ci gaba da kashe bayin Allah.
Jaridar ta ce a 'yan makonnin nan hare-haren Boko Haram sun karu musamman a kauyuka da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ba safai ake samun labarin wannan ta'asa cikin lokaci ba, sai an dauki kwanaki masu yawa kafin labaran hare-haren su bayyana. Hakan dai na zuwa ne bayan da a watannin baya, gabanin zaben Najeriya sojojin kasar suka samu gagarumar galaba a kan masu tayar da kayar bayan.
Jaridar ta kara da cewa a makon da ya gabata Shugaban Chadi Idris Deby ya yi ikirarin cewa Boko Haram ta maye gurbin shugabanta Abubakar Shekau da wani mai suna Mahamat Daoud. Amma kwanaki kalilan bayan wannan ikirarin sai wani sauti ya bayyana dauke da muryar Shekau yana jaddada cewa har yanzu shi ne jagoran 'yan tarzoman.
Sabon wa'adin mulki na uku a Burundi
A karshe sai jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Burundi tana mai cewa a wani mataki na ba-zata, a ranar Alhamis an yi bikin rantsar da shugaban kasar Pierre Nkurunziza a sabon wa'adin mulki na uku, mako guda gabanin lokacin da aka tsara rantsar da shi. Da farko dai an shirya rantsar da shi din ne a ranar 26 ga watan nan na Agusta. Shi dai shugaban ya lashe zaben kasar mai cike da takaddama, da kimanin kashi 69 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada, zaben kuma da 'yan adawa suka kaurace masa.