1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu na adawa da karin sojoji

Zainab Mohammed AbubakarAugust 13, 2016

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi adawa da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na tura karin dakarun kiyaye zaman lafiya kimanin 4,000 daura da wadanda ke kasar a yanzu.

https://p.dw.com/p/1Jhbd
Südsudan UN denken über Verstärkung von Unmiss nach
Hoto: Reuters/A. Ohanesian

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin tura karin sojojin kiyaye zaman lafiya 4,000 zuwa babban birnin kasar Sudan ta Kudu watau Juba.Dakarun za su kasance bangaren sojojin MDD da ke girke a kasar. Kwamitin sulhun dai ya yi barazanar daukar matakin kakabawa Sudan ta kudun mai fama da riginmu, takunkumi sayen makamai idan har ta ki bada hadin kai kan wannan shiri.

Kudurin da Amirka ta gabatar dai, ya samu amincewar wakilai 11 na kwamitin sulhun, tare da kin bayyanan kasashe hudu da suka kunshi Rasha da China da Venezuela da Masar. Jakadan Amirka kan harkokin siyasa a MDD David Pressman ya bayyana wasu daga cikin aiyyukan sojojin:

" Kamar dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD da a yanzu haka ke girke a Sudan ta Kudu, wadannan karin sojoji zasu yi aiki a karkashin dokar sashi na 7, wanda ke basu ikon amfani da duk wata hanya na sauke nauyi da ya rataya a wuyansu. Aiyyukansu zai kunshi kare lafiyar fararen hula da kula da hakkin bil'Adama tare da samar da hanyoyin kai kayayyakin agaji a inda ake bukata".Gwamnatin Sudan ta kudun dai ta nuna rashin amincewarta da bayyanar karin wadannan dakaru a doron kasarta, duk kuwa da rayuka da suka salwanta sakamakon fada a watan da ya gabata.