Sudan ta kudu na janyewa daga fagen daga
April 23, 2012Talla
Gwamnatin Sudan ta kudu ta bayyana cewa sojojin ta na ci gaba da picewa daga yankin da suka maye wanda ya jawo fada tsakanin ta da Khartum. Ministan yada labaran a Juba yace dakarun na su na janye, kuma zai dauke su kwanaki ukku kafin su kammala picewa daga yankin Heglig da ake taƙaddama a kansa. Ƙarin haske kan janyewar ya zo ne a dai-dai lokacin da shugaban ƙasar Amirka Barack Obama ya buƙaci Khartum da Juba su shiga tattaunawa don war-ware rikicn.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Zainab Muhammed Abubakar