1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu ta bukaci a dage zaben kasar

Yusuf BalaFebruary 14, 2015

Cikin tsare-tsaren da aka fitar tun a farkon wannan wata Kiir da Machar sun amince kan yarjejeniyar raba madafun iko inda ake fatan su kai ga cimma matsaya ta ƙarshe a watan Maris.

https://p.dw.com/p/1Ebml
Bildkombo Südsudan Riek Machar und Salva Kiir
Hoto: Getty Images/Zacharias Abubeker/Ashraf Shazly/Montage

Ƙasar Sudan ta Kudu ta buƙaci a dage zaɓen ƙasar da aka tsara yi a watan Yuni sannan majalisar zartarwar ƙasar ta buƙaci majalisar dokoki ta ƙara wa'adin mulkin shugaba Salva Kiir a dai dai lokacin da ake ci gaba da taƙaddama kan harkokin raba madafun iko tsakanin shugaba Kiir da tshohon mataimakinsa Riek Machar.

Dubban mutane dai suka hallaka yayin da sama da miliyan ɗaya aka tilasta musu kaurace wa muhallansu bayan da fada ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu masu adawa da juna a watan Disambar 2013 a wannan ƙasa da ke zama sabuwa da samun 'yancin kanta cikin ƙasashen duniya.

Michael Makuei mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ta Sudan ta Kudu ya ce za a gabatar da wannan buƙata ta neman karin wa'adin mulkin shugaba Kiir a gaban majalisa a ranar Talata mai zuwa inda ya bayyana kyakkyawan fata na ganin 'yan majalisar sun amince.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Abdurahamane Hassane