1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan Ta Kudu ta ce a shirye take ta yi sulhu da Sudan

May 10, 2012

Sudan ta gindayawa Sudan Ta Kudu sharaɗin warware matsalar tsaro gabannin komawa ga teburin sulhu.

https://p.dw.com/p/14tZ1
(FILE) A file picture dated 19 January 2010 shows Sudanese President Omar el Bashir (R) and First Vice President and President of the Government of Southern Sudan, Salva Kiir Mayardit (L), participating in celebrations marking the 5th anniversary of the signing of the Comprehensive Peace Agreement (CPA) in Yambio, Sudan. Omar el Bashir has won the country's first multiparty elections in 24 years, election officials said on 26 April 2010. The polls are supposed to usher in a new era of democracy in Sudan, which is recovering from a decades-long civil war between the north and south. EPA/TIM MCKULKA - UNMIS - HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugaba El Bashir na Sudan da Salva Kiir na Sudan Ta KuduHoto: picture-alliance/dpa

Sudan Ta Kudu ta faɗi a wannan Alhamis cewar a shirye take ta koma ga tattaunawa da Sudan a kowane lokaci domin warware batutuwa daban daban da sassan biyu ke taƙaddama akan su. Sai dai kuma Sudan ta ce ba za ta shiga wata tattaunawa ba - hai sai dukkan ɓangarorin biyu sun shawo kan taƙaddamar tsaron dake tsakanin su. Ƙasashen biyu dai suna ta sa-in-sa a tsakanin su akan man fetur, da batutuwan da suka shafi tsaro, abubuwan da kuma suka ruruta wutar rikicin kan iyakokin a tsakanin ƙasashen biyu tun kimanin wata guda kenan.

Tuni ƙasashen duniya suka bayyana fargaba game da yiwuwar su koma ga yaƙi bayan kawo ƙarshen yaƙin basasar daya kai su ga rabewa. Sai dai kuma a cewar Andrew Ata Asamowa na cibiyar nazarin harkokin tsaro dake birnin Pretoria na ƙasar Afirka Ta Kudu, idan har zargin ƙaddamar da hare haren bama bamai ya tabbata a tsakanin Sudan da Sudan Ta Kudu, to, kuwa za su fuskanci takunkumi:

"Ya ce idan har rahotannin ƙaddamar da hare haren bama bamai suka tabbata, to, kuwa akwai yiwuwar kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙungiyar tarayyar Afirka su yi zaman ɗaukar matakin sanyawa ƙasashen takunkumi."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu