Sudan ta kudu ta dakatar da aikin kungiyar CICR
February 1, 2014Wannan kungiya da kanta ne ta bayar da wannan labarin a yau din ga kampanin dillancin labarun kasar Faransa, inda su ke cewa sun samu wata wasika ce,daga komitin dake kula da harkokin agaji na kasar ta Sudan ta Kudu inda ya sanar da su cewa daga yau daya ga wannan wata na Febreru, sun dakatar da ayukan su a wannan kasa.
Sai dai duk da cewa an rufe wannan kungiya amma ma'aikatan ta a kalla dari bakoye dake ayuka a sassa daban daban na kasar, zas u cigaba da zama a offishin wannan kungiya.
Wannan kungiya dai ta bayar da agajin ga a kalla mutane Milian daya da rabi a yankuna da dama na kasar ta sudan ta kudu, a fannoni da dama, da suka hada da batun kiwon lahiya, tallafi ga abinci, da ma na irin shukawa ko kuma ma kan batun tsarkakekken ruwan sha.
Ana sa ran soma tattaunawa tsakani a 'yan kwanaki masu zuwa tsakanin offishin Ministan harkokin wajan kasar, da 'yan kungiyoyin kula da agaji na kasa da kasa.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Zainab Mohamed Abubakar