Sudan ta Kudu ta fara fidda mai ta Sudan
April 14, 2013Karamin minista a ma'aikatar Awad Abdul Fatah ne ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP a wannan Lahadin inda ya ce da yammacin jiya ne man ya fara isa Sudan to sai dai man da aka tura daga Sudan ta Kudun bai da yawa, hasali ma dai bai wuce wani mataki na gwaji ba.
Fara tura man dai na jiya ya biyo bayan cigaba da hakar danyen mai da aka yi kwanaki takwas din da su ka gabata a rijiyoyin man da ke Thar Jath bayan da aka rufe su kimanin shekara gudan da ta gabata bayan rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin kasashen biyu dangane da harajin da Sudan za ta rika karba a hannun Sudan ta Kudu saboda amfani da wani yanki na kasar ta wajen fidda man fetur din ta.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da shugaba Umar Hassan el-Bashir ya kai ziyara Sudan ta Kudu inda ya gana da shugaba Salva Kiir, lamarin da ya sa ake ganin hakan zai taimaka wajen farfado da dangantakar da ta yi tsami tsakanin bangarorin biyu.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu