Sudan ta Kudu tana da ja kan yarjejeniyar zaman lafiya
August 27, 2015Gwamnatin Sudan ta Kudu ta nuna rashin amincewarta da wasu sharudda 16 na yarjejeniyar zaman lafiyar da kasashen duniya suka tilasta wa Shugaba Salva Kiir saka hannu a kanta a ranar Larabar Jiya a birnin Adis Ababa. Gwamnatin kasar ta Sudan ta Kudu ta bayyana wannan matsayi nata ne a cikin wata takarda da ta mika wa mai shiga tsakani cikin wannan rikici na kasar ta Sudan ta Kudu a wannan Alhamis.
Daga cikin matakkan da gwamnatin kasar ta Sudan ta Kudun ta ce ta na da ja da su sun hada da matakin mallaka wa 'yan tawayen kasar mukamin mataimaki na farko na shugaban Kasa da yarjejeniyar ta tanada .
A ranar Laraba ne dai a bisa matsin lambar manyan kasashen duniya, Shugaba Kiir ya sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiyar wacce ke da burin kawo karshen yakin basasa da kasar ta kwashe kusan shekaru biyu tana fama da shi.