1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kin mutumta yarjejeniyar tsagaita a Sudan

May 4, 2023

Ana ci gaba da gwabza fada a Khartum fadar ayin da aka kwashe kimanin kwanaki 20 da barkewar rikicin Sudan bangarorin da ke gwabza fada sun ci gaba musayar wuta a birnin Khartoum.

https://p.dw.com/p/4QuQh
Hoto: Mohamed Nureldin Abdallah/REUTERS

Sojojin da ke biyayya ga manyan hafsoshin sojan Sudan biyu da ke kokawar iko, sun sa kafa sun shure yerjejeniyar tsagaita wutar da aka tsawaita izuwa ranar 11 ga watan Mayu domin samun damar isar da kayan agaji. Masu aiko da rahotanni sun ce an ji karar fashewar bama-bamai da kuma manyan bindigogi, yayin da fadan ke ci gaba da jefa al'umma cikin kuncin rayuwa na katsewar wutar lantarki da ruwan sha da kuma hauhawar farashi da ma karancin man fetur.

Babban kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk ya yi tir da yadda wani jirgin sojoji ya yi luguden wuta a kan wani asibiti da kuma yadda dakarun RSF ke kai hare-hare a unguwannin fararen hula. A yankin Darfur kuwa inda fararen hula suka dauki makamai domin shiga yakin kuwa, kungiyoyin agaji sun nuna takaicinsu kan yadda fada tsakanin kabilun yankin ya yi ajalin mutane 191 tare kuma da kone gidaje masu yawa.