Zanga- zangar 'yan adawa a Sudan
January 11, 2019Talla
A cikin wata sanarwa da hadin gwiwar kungiyoyin suka bayyana sun ce za su yi mako daya jere na gangami a ckin garuruwa da kauyuka domin tilasta wa shugaba Omar al-Bashir yin marabus. Yau kusan makonnin uku ke'nan da gwamnatin ta Sudan take fuskantar borai mafI muni tun daga shekara ta 1989 lokacin da Al Bashir ya karbi mulki. Kungiyar kare hakin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce mutane 40 suka mutu a zanga-zangar da farko ta neman a rage frashin kudin biredi ce kafin ta rikide ta koma ta siyasa.