'Yan adawa a Sudan sun ki yarda da tayin sojoji
June 5, 2019Sai dai kuma yinkurin da wasu kasashen duniya suka yi a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na daukar kudi yin tir da Allah wadai da kisan fararan hulan a Sudan ya ci tura, bayan da kasashen Chaina da Rasha suka hau kujerar naki a taron kwamitin da ya gudana a yammacin jiya Talata.
Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman nasa ne da nufin daukar mataki biyo bayan kisan masu zanga-zangar neman sauyi da jami'an tsaron kasar ta Sudan suka yi a birnin Khartoum inda a yanzu adadin mutanen da suka mutu a cikin lamarin ya kai 40.
Kasashen Amirka da Birtaniya da Norway sun soki a jiya Talata lamirin shugabannin hukumar mulkin sojan kasar ta Sudan da aniyarsu ta shirya zabuka da kansu, inda suka yi kira da su kafa gwamnatin rikwan kwarya ta fararan hula, wacce za ta shirya zabukan a cikin kwaciyar hankali da adalci.