Sudan za ta katse hulɗa da Sudan ta Kudu
June 8, 2013Talla
Sanarwa wace Gidan Rediyon na ƙasar ya bayyana ta zo ne makonnin biyu, bayan da aka sake cimma yarjejeniyar fiton da aka dakatar a can baya tsakanin ƙasashen biyu.
Sanarwa ta ce shugaban ya bai wa ministan harkokin man fetur na ƙasar ummarnin dakatar da fiton daga bakin gobe Lahadi. Ko da shi ke ba a bayyana dalilan ɗaukar matakin ba, amma da allama ba zai rasa nasaba ba ,da goyon bayan da Sudan ɗin ke zargin Sudan ta Kudu na bayar wa ga 'yan tawayen Kordofan ta Kudu. Wanda tun da fari shugaban ya yi barazanar cewar zai dakatar da fiton inda hukumomin Juba suka ci-gaba da ba su goyon baya.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman