Sudan za ta samu taimakon miliyan 1500
June 20, 2023Kasar Jamus da ke sahun wadanda suka shirya taron neman tallafin a Geneva ta ce za ta ba wa Sudan miliyan 200 na Euro kan nan da shekara ta 2024, yayin da Kungiyar Tarayyar Turai ta yi alkawarin ba da Euro miliyan 190. Wannan yana nufin cewa kaso daya cikin biyu na jimillar kudin da hukumomin agaji suke bukata kawai za a iya samu, don tallafa wa 'yan Sudan miliyan 25 da ke dogara kan taimakon jin kai.Sai dai taron agajin ya gudana ne a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki uku a Sudan ya fara maido da kwanciyar hankali a birnin Khartoum. Rahotannin sun nunar da cewa an daina kai hare-hare ta sama a babban birnin Sudan inda miliyoyin mazauna ke rayuwa a karkashin tsananin zafi. Fiye da mutane 2,000 ne suka mutu a cikin watanni biyu da aka shafe ana yaki tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhane da Janar Mohamed Hamdane Daglo.