Sudan za ta sauya tsarin mika mulki ga farar hula
January 20, 2022Hukumomin Sudan sun amince da bukatar Amurka na sauya takardun yarjejeniyar mika mulki a hannun farar hula a kasar. Sanarwa da mahukuntan na Sudan karkashin majalisar jami'an da ke gudanar da shugabanci wadda Janar Abdel Fattah al-Burhan ke jagoranta ta ce hakan ya zama wajibi domin takardun su tafi daidai da halin da kasar ke ciki yanzu haka.
Wannan na zuwa ne a yayin da ofishin jakadancin Amurka a birnin Khartoum ya sanar a Alhamis din nan cewa Amurka ba za ta dawo da ba Sudan tallafin kudi ba har sai an kawo karshen tashin hankalin da ke wakana kuma an dawo da gwamnati da farar hula ke jagoranta a kasar.
A gefe guda kuma masu zanga-zanga sun sake yi wa sojojin Sudan bore a wannan Alhamis domin nuna fushinsu kan yadda jami'an tsaro ke kashe masu boren tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar da ta gabata.