Suka bisa kone al-Kassasbeh da IS ta yi
February 4, 2015Talla
Jami'ar ta Azhar dai na zaman wata babbar cibiyar nazarin addinin Musulunci, ta ce sanya al-Kassasbeh cikin keji tare da banka masa wuta da ransa da 'yan IS din suka yi babban rashin imani ne. A jawabin da ya yi shugaban jami'ar ta Azhar Ahmed al-Tayib ya ce abin da 'yan IS din suka aikata babban kuskure ne da ya sabawa ka'idojin addinin Islama da kuma koyarwar ma'aiki. Ya kara da cewa Musulunci yana hana kashe wadanda basu-ji-basu-gani ba koda kuwa lokacin yaki ne, musamman ma yi musu kisan wulakanci.
Mawallafiya: Lateefa Msutapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal