Firaministan Habasha ya ziyarci Sudan don yin sulhu
June 7, 2019Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya sauka a wannan rana ta Juma'a a babban birnin Khartum na kasar Sudan, a wani yunkurin da yake na shiga tsakani don sasanta bangarorin da ke jayayya da juna na soja da fararen hula.
A ziyarar, Abiy Ahmed zai gana da majalisar mulkin sojan Sudan ta rikon kwarya, kana zai kuma yi wata tattauana wa da ‘yan fafatuka a daidai lokacin da daukacin kasashen duniya ke yin Allah wadarai da matakin sojan kasar na kisan masu bore da zanga-zanga.
Yanzu hakan dai manyan titunan babban birnin kasar Khartoum na ci gaba da kasancewa a kufai, kana kuma wasu sauran shagunan na ci gaba da zama a rufe, inda rahotanni suka ce sojoji ne kawai ake iya gani a ko ta ina.
Akalla mutane 113 ne wasu rahotanni ke cewa sojan sun hallaka, sakamakon kakkabe masu zanga-zangar da suka yi share wuri zauna a farkon wannan makon, lamarin da kuma ya kara janyowa majalisar sojan yankon jini.