Switzerland ta yi tayin sulhu a Kamaru
June 27, 2019Talla
A cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Switzerland ko Suisse ta fitar a ranar Alhamis, ta ce bangarori da dama ne suka bukaci gwamnati ta jagoranci wata tattauanawar sulhu tsakanin bangarorin da ba sa jituwa, zuwa ga wata tattaunawa ta hakika domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Rikicin da 'yan awaren suka shafe watanni suna tafkawa da bangaren gwamnatin Kamaru ya lamshe rayukan jama'a fiye da dubu 1.800, baya ga haddasa kaurar jama'a daga gidajensu akalla dubu 530.000.