Ta'addancin 'yan IS na kara kamari
October 9, 2014Talla
A dai dai lokacin da Amirka ke ci gaba da jagorantar yin barin wuta a kan yankunan da 'yan ta'addan kungiyar IS ke da karfi a kasashen Siriya da Iraki, kungiyar na kara mayar da hankalinta kan iyakar Siriya da Turkiya inda rahotanni ke nuni da cewa sannu a hankali tana samun galaba, ab un da ya janyo bukatar samar da dakarun da zasu fafata da IS din ta kaa maimakon yakarta ta sama kawai.