1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'asar 'yan bindiga a Sudan ta Kudu

Abdul-raheem Hassan
October 10, 2016

Hukumomin soji da na 'yansanda a Sudan ta Kudu, sun tabbatar da mutuwar mutane 30 a wasu hare hare da 'yan bindiga suka kaddamar a kan wasu motocin fasinja.

https://p.dw.com/p/2R5uB
Südsudan Opposition Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Kakakin rundunar 'yansanda a Juba babban birnin Sudan ta Kudu Justin Boula, ya ce lamarin ya faru ne a farkon mako yayin da wasu 'yan bindiga suka yi wa motoci uku da ke kan hanyar su ta zuwa Yuganda kwanton bauna inda suka kashe mutane tara wasu mutane shida kuma suka sami raunin harsahi.

A wani lamari irin wannan ma dai, Kakakin rundunar soji da ke aikin kwantar da tarzoma a kudu maso yammacin kasar, Lul Ruai Koang, ya ce da farko dai maharan sun tare wata motar safa ce a kusa da garin inda suka kashe mutane 21 nan take ciki har da kananan yara sha biyar sannan suka raunata wasu mutune 20 a yayin da su ka bankawa motar wuta.

A baya dai ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu, ya koka kan yadda ake gallazawa fararen hula a kasar, baya ga mutane miliyan biyu da rabi da rikicin siyasa ya tilastawa gudun hijira.