Takkadama tsakanin Falasdinawa da sojan Isra'ila
May 5, 2019Mutumin dan shekaru 58 ya mutu ne bayan da aka kaishi asibiti sakamakon munanan raunukan da ya samu saboda tarwatsewar rokar a gidansa.
Wannan dai shi ne Bayahuden Isra'ila na farko da ya rasu tun bayan da aka shiga wani yanayi na rikici mai tsanani tsakanin Kungiyar Hamas mai rike da iko a yankin Gaza da kasar Isra'ila.
Har yanzu Isra'ilar na ci gaba da ruwan bama-bamai kan zirin Gaza a yayain da ita kuma kungiyar Hamas ta ke ci gaba da cinna rokoko kan Isra'ila.
Tuni Kungiyar Tarayyar Turai ta kirayi Isra'ila da ta dakatar da ruwan bama-bamai da harba rokoki kan zirin Gaza nan take, a daidai lokacin su kuma hukumomin kiwon lafiya a yankin Gaza suka tabbatar da fara samun asarar rayukan mutane ciki har da wata karamar yarinya.
Sai dai sojojin Isra'ila sun kare kansu na kai hare-haren da nufin daukar fansa kan rokoki akalla 400 da suka ce Faladsinawa sun harba daga zirin Gaza.