Malamai masu koyar da ilmuka na addini na amfani da kafafen sadarwar zamani wajen yada fatawowi, inda miliyoyin mabiyansu ke amfanuwa da su a kasashen duniya. Shirin wannan lokaci ya dubi yadda ake samun matsalar zafafa kalamai ne a tsakanin maluman addini ta kafofin sada zumuntan na zamani.