Shirin ya dubi irin yadda kasashen Afirka da suka hada da Najeriya da Nijar da Senegal suka rabauta da masallatai da makarantu da wasu kasashen musulmi irin su Saudiyya da Turkiyya da Iran suka samar. Wasu na ganin hakan wata hanya ce ta cusa wasu akidu. A saurari shirin don jin karin batutuwa.