1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiya na taimakon nakasassu a Nijar

Salissou Kaka/LMJJuly 27, 2016

A Jamhuriyar Nijar wata kungiya ta mabiya addinin Kirista ta dukufa wurin kawo sauyi a rayuwar nakasassu, inda ta bude musu wani gida na musamman domin koyar dasu sana'o'in hannu.

https://p.dw.com/p/1JWg0
Koyar da nakasassu sana'o'in hannu a Nijar
Koyar da nakasassu sana'o'in hannu a NijarHoto: picture-alliance/dpa

Sana'o'in da wannan kungiya take horas da nakasassun dai sun hadar da dinki da zane-zane da wasanin motsa jiki, kana a karshe ta yaye su ta kuma basu jari da kayan aiki domin daukar nauyin kansu da kansu. Wannan cibiya dai mai suna Centre Hosana nan ne gidan koyar da ayukan hannu ga nakasassu da kungiyar mabiya addinin Kiristan ta ONG HOSANA ta samar. Wadanda ke cin gajiyar wannan shiri dai sun hadar da maza da mata da ke dauke da naksa, kama daga guragu da kurame da makafi da kutare, wadanda adadinsu ya kai mutane 100. Shugaban wannan cibiya Sulaimane Ibrahim da ke da kimanin shekaru 35 a duniya reshen jihar Maradi ya shaida wa DW cewa sun yanke shawarar taimakwa nakasassun ne domin magance zaman banza da kuma barace-barace. Dukan wadanan ayyuka dai kungiyar na koyar dasu ne tare da hadin kan kungiyar nakasassu ta jihar ta Maradi. Malama Ramma ita ce shugabar mata ta kungiyar nakasassun a birnin Maradi ta kuma ce sabon sauyi ne ya samu a rayuwarsu. Abun mamaki duk da nakasar da ke garesu bata hanasu gudanar da ayyukan hannun ba. Ko bayan sana'o'in hannun dai wanan kungiya ta HOSANA na koyar da nakasassun wasanin motsa jiki irinsu kwallon kafa.