Takaddama tsakanin Isra'ila da Turai akan Falasdinu
December 10, 2012Firayiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yayi watsi da sukar da al'ummomin kasa da kasa ke yiwa kasar sa game da shirin gina karin matsugunan Yahudawa 'yan kama-wuri zauna a yankin gabashin birnin Qudus da Isra'ilar ke ci gaba da mamaya. A lokacin daya ke magana da manema labarai na kasashen ketare a wannan Litinin, Netanyahu ya bayyana mamakinsa game da sukar da shirin ke sha domin kuwa a cewarsa bai fahimci madogarar jama'a ba akan batun. Ya ce idan har za'a iya samun kasar Falasdinu a tsakanin zirin Gaza da gabar tekun Jordan, to, kuwa babu wata matsala idan aka hade yankin Maalah Adumim da birnin Qudus.
A dai wannan Litinin ne kungiyar tarayyar Turai ta bayyana takaicinta dangane da shirin da Isra'ila ta bayyana na kara samar da matsugunan Yahudawa a yankunan Falasdinawan da take ci gaba da mamaya, bayan da Falasdinu ta yi nasarar samun kujerar 'yar kallo a zauren Majalisar Dinkin Duniya. A cikin wata sanarwar da taron ministocin kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai mai kasashe mambobi 27 suka fitar, sun bayyana takaici tare da yin kakkausar suka ga matakin Isra'ila na shirin fadada matsugunan Yahudawa a gabar tekun Jordan ciki harda gabashin birnin Qudus, musamman kuma shirinta na baya bayannan mai lakabi da E1, wanda a karkashinsa za ta gina karin matsugunai 3,000. a yankunan Falasdinawa.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal