Saudiyya ta kori Jakadar Kanada daga kasarta
August 6, 2018Talla
Saudiyya ta kori jakadar kasar Kanada dangane da abin da ta kira katsalandan a al'amuranta na cikin gida.
Hukumomin dai sun baiwa jakadar ta Kanada wa'adin sa'oi 24 ta tattara ya nata ya nata ta bar kasar.
Hakannan kuma Saudiyya ta kira jakadanta a birnin Ottawa na kasar Kanada ya dawo gida.
Kasar ta Saudiyya ta kuma baiyana katse dukkan wasu sabbin zuba jari da kuma cinikayya da Kanada.
Wannan dambarwa dai ta biyo bayan wasu bayanai ne da ministar harkokin wajen Kanada Chrystia Freeland ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ke cewa Kanada ta yi mamaki yadda hukumomin Saudiyya suka kama Samar Badawi kanwar Ra'if Badawi wani mawallafi a shafin Internet wato Blog a turance wanda ake tsare da shi tare da wata 'yar fafutuka Nassima al Sada.