Tarihin sabuwar Jagorar CDU
December 8, 2018Sabuwar jagorar ta jam'iyyar CDU har wa yau dai mace Annegret Kramp Karrenbauer rikakiyar 'yar darikar Roman Katolika ce 'yar shekaru 56 da haifuwa wace ake yi wa la'akabi da sunan AKK ko mini Merkel ganin irin yadda take zaman babbar ta hannun dama kana ta kusa da shugabar gwamnatin Jamus wacce za ta gada watau Angela Merkel. Ta dai doke hamshakin attajirin nan kuma lauya, Friedrich Merz da kuri'u 517 yayin da shi yake da kuri'u 482 a zagaye na biyu na zaben kafin tun da farko dan takarar guda Jens Spahn ya dangana ya janye. Annnegret Kramp Karrenbauer wacce ta fito daga yankin yammacin Jamus daga Jihar Saarland da ke makobtaka da Faransa wacce ta karanci kimiyyar siyasa da harkokin shari'a ta rike mukamai da dama na siyasa a cikin shekaru 12 kama daga ministan kula da jin dadin iyali da ilimi da ministan al'adu da na aiki a Jiharta. Kuma ita ce mace ta farko da ta rike matsayin minista cikin gida a Jihar ta Saarland kafin a shekara ta 2011 ta zama firaministan jihar bayan da firimiyan jihar Peter Müller ya sauka daga mukamin sannan a cikin watan Faibrairu da ya gabata ta ajiye matsayin don zama magatagardar jam'iyyar CDU.
Tana da irin ra'ayi guda da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Ana dai yi ma ta kallon mai irin ra'ayi daya da Angela Merkel sai dai duk da irin biyayyar da take yi mata bai hana suna da sabanin ra'ayi ba a kan wasu batutuwa da suka hada da auren jinsi da zubar da ciki da batun 'yan gudun hijira wanda a shekara ta 2015 ta nuna dari-darinta da siyasar shugabar gwamnatin ta karba 'yan cirani. Kamar Angela Merkel mace ce da ke son bin hanyoyin lalama na tattaunawa domin samun masalha a kan haka ne ma ta ce za ta kara janyo a jiki abokanan takararta da ta kayar 'yan adawar Merkel domin dinke duk wata baraka da ka iya tasowa a cikin jam'iyyar ta CDU kamar yadda ta taka rawa a baya-baya nan wajen kula yarjejeniyar kafa gwamnati hadaka tsakanin CDU da ja'miyyar masu ra'ayin gurguzu ta SPD.
Kalubalen da ke a gaban sabuwar shugabar jam'iyyar CDU
Annegret Kramp Karrenbauer mace ce da ba ta da daurin kai wani lokacin ta kan hau babur don shiga gari haka kuma tana zuwa don buga wasan kwallon kafa ko kuma wasan gora. Tana da ya'ya guda uku mijinta Helmut inijiniyar hako ma'adinai da ya bar aiki domin kula da iyali har kullum yana goyon bayan matarsa a ciki ayyukanta na siyasa. Sabuwar Jagorar ta CDU wadda ake ganin tamkar ita ce 'yar takara CDU a zaben Jamus na gaba tana da mayan manufofin a gabanta wadanda ta bayyana a lokacin da take yin jawabi a game da sh'anin tsaro da kula da kare muhali da batun wasu sauye-sauye na zamani. A halin da ake ciki zaben nahiyar Turai dai da za a gudanar a shekarar badi shi ne zai zame mata zakaran gwajin dafi na farko.