Takun saka tsakanin Masar da Habasha, da ke aikin gina dam a kan kogin Nilu
June 12, 2013Matasa masu fafutuka sun yi ta ta da tsimin juna a yayin cincirindon nuna fushi da suka yi a farfajiyar ofishin jakadancin Habasha da ke Masar, suna masu tofin Allah tsine da matakin da suka ce na takalar fada ne kasar ta Habasha ta dauka.
"Wannan mataki zai katse kyakkyawar alaka da ke tsakaninmu ta tsawon shekaru aro-aro muddin kuka yi kunnen kashi kuka nemi yi mana kanshin mutuwa ta hanyar datse mana ruwan kogin Nilu."
Mamona ba za su lamunta ba
Wani manomi da ya siffanta fara gina dam din da ayyana yaki kan kasar Masar ya yi kira ga 'yan kasar da su daura damara tinkarar wannan kalubale;
"Wannan batu ne da ya shafi ruwan kogin Nilu wato rayuwarmu da ta 'ya'yanmu idan ba za a iya sasantawa ta hanyar lumana ba, to ba abin da ya rage mana sai daura damarar yaki."
Wani kwararre kan gina dama-dami kuwa cewa yake ko da mahukuntan Masar za su mika kai bari ya hau, don kare bukatunsu na siyasa, to fa manoma da abin zai shafa kai tsaye ba za su nade hannu suna gani a yi musu sakiyar da ba ruwa ba.
"Ba karamin lahani gina wannan dam zai yi wa Masar ba. Zai busar da kadada miliyan biyar. Don haka manoman Masar za su yi gaban kansu su je su rusa dam din ko da sama da kasa ne za su hadu.'
Martanin 'yan adawa
A yayin da mahukunta da yawancin 'yan kasar ke mai da irin wannnan kakkausan martani su kuwa jam'iyyun hamayya da suka dora alhakin jawo wa kasar Masar reni kan jam'iyyar 'Yan uwa Musulmi da suke zarginta da rashin iya mulki kira suka yi da a yi taka tsantsan;
"Fadar shugaban kasa ta kasa tsinana komai in banda kurari da nuna isa. Wannan zai kai mu ya baro ne. Kamata ya yi mu bi matakan tuntuba da lallama da kuma kyautata alakarmu da kasashen Afirka, wadanda a baya muke musu ganin ganga ba rufi, domin duk wani matakin nuna isa ko amfani da karfi da za mu yi, kasar Habasha kan iya kaimu gaban kwamatin tsaro na duniya-lamarin da ba zai yi mana kyau ba."
Komai dai ake ciki ko shakka babu mahukuntan na Masar tare da sauran al'ummar kasar gami da 'yan hamayya na bukatar ajiye sabanin da ke tsakaninsu don tunkarar wannan gagarum kalubalen da ke zama irinsa na farko da kasar ta Maser ke fuskanta tun bayan yakin da ta yi da Isra'ila.
Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa
Mawallafi: Mahmud Yahaya Azare
Edita: Halima Balaraba Abbas