Takun saƙa ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa a Liberia
October 16, 2011'Yan Liberia sun fara nuna fargaba game da takun saƙa da aka fara fiskanta tsakanin 'yan takara da suka fafata a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana ranar talata da ta gabata. Tara daga cikin jam'ian adawan ƙasar sun ƙi amincewa da ƙwarya-ƙwaryar sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta bayar, a inda ta nuna cewa shugaba mai barin gado Ellen Johnson- Sirleaf ta lashe kashi 44,6% na ƙuri'un da aka kaɗa. Zaɓen shugaban ƙasar dai shi ne irinsa na biyu da aka shirya tun bayan yaƙin basasa na liberia wanda ya haddasa mutuwar mutane kimanin 250. 000.
Waɗanda suka ƙalubalanci Johnson- sirleaf ciki har da Winston Tubman ya bukacin wakilan adawa da su ƙaurace ma zaman tantance sakamakon zaben da ake yi bisa zargin tafka magudi. Sai dai wani ƙusa a jam'iyar Up da ta tsayar da shugaba sirleaf, ya ce wacce ke cikin waɗanda suka lashe kyautar Nobel ta bana, ba za ta sami yawan kuri'un da za su bata damar lashe zaɓen tun a zagayen farko ba.
Ranar takwas ga watan nowamba mai zuwa ne idan Allah ya kai mu za a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen shigaban ƙasa tsakanin Ellen Johnson- sirleaf na jam'iyar Up da kuma Winston Tubma na jam'iyar CDC.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu
AFP 161132 GMT OCT 11