Takunkumi ga Sudan ta Kudu
September 2, 2016Kwamitin ya ce in har gwamnati taki amincewa da kara tura dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar 4,000 zuwa kasar to tabbas za ta fuskanci takunkumi. Ziyarar ta Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkiin Duniyar dai, za ta mayar da hankali ne ga yunkurin majalisar na sake tura dakarun wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudun domin kare rayukan fararen hula da ke fuskantar hare-hare da fyade daga dakarun gwamnati. Mahukuntan kasar ta Sudan ta Kudu dai sun bayyana wannan yunkuri na Majalisar ta Dinkin Dunyia da wani sabon nau'i na yi musu mulkin mallaka. Ana sa ran wakilan Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya za su gana da Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudun, da nufin tilastawa bangarori biyu da ke yakar juna a kasar komawa domin yin amfani da yarjejeniyar sulhu da aka cimma a shekarar da ta gabata ta 2015.