Takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kan Taliban
July 16, 2011A yunƙurinta na neman sassantawa da ƙungiyar wacce haɗin kan ƙungiyoyin ƙawance a ƙarƙashin jagiorancin Amurka suka tumɓuke a shekarar 2001. A yanzu haka dai Ƙasar Jamus na riƙe da muƙamin shugabancin karɓa-karɓa na kwamitin sulhun, kuma wakilin ta a Majalisar Ɗinkin Duniya Peter Wittig ya ce wannan yunƙuri ya nuna cewa alummar ƙasa da ƙasa na goyon bayan duk wani yunƙuri na ƙaddamar da tattaunawa tsakanin shugabanin ƙungiyar masu matsakaicin ra'ayi da kuma gwamnati a Kabul. Shi ma dai Shugaban na Afghanistan, Hamid Karzai na cigaba da nasa ƙoƙarin wajen ganin ɓangarorin sun zauna bisa teburin tattaunawa. Wannan mataki na cire sunayen, ya rage adadin shugabanin ƙungiyar ta Taliban, waɗanda aka sanyawa takunkumi zuwa 123. Hakanan kuma, dakarun ƙetare dake aiki a Afghanistan na fatar kammala janyewa gabaki ɗaya a shekarar 2014 domin miƙa alamurar tsaron ƙasar zuwa ga jami'an tsaro da 'yan sandan ƙasar
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Ahmad Tijani Lawal