Taliban ta kashe sojojin Afghanistan
April 26, 2018Talla
Rahotannin da ke fitowa daga Kabul babban birnin kasar Afghanistan, na cewa akalla sojojin gwamnati 23 ne suka mutu a wasu hare-haren da mayakan Taliban suka kaddamar cikin lardunan kasar hudu. Wannan labarin ya fito ne bayan wata sanarwar kungiyar ta Taliban a jiya Laraba. Haka nan sanarwar ta ce akwai ma wasu jamai'an 'yan sanda 9 da suka salwanta tare da wasu mayakan kungiyoyin sa kai.
Kashe-kashen sun auku ne lokacin wani hari da mayakan suka kai a gundumar Almar da ke arewacin Faryab da misalin karfe takwas na yammacin jiyan agogon kasar. A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne dai shugaba Ashraf Ghani, ya kara wa'adin tayin sulhu da ya yi wa mayakan na Taliban, sai dai fa sun yi watsi da hakan.