Taliban ta yi kisa a taron maulidi
December 1, 2017Talla
Rahotannin dake fitowa daga kasar Pakistan, na cewa wasu mayakan Taliban sun kashe mutane tara yayin kuma da wasu da dama suka jikkata. Lamarin dai ya faru ne a wata makarantar dake arewa maso yammacin Peshawar, lokacin da matasa ke bikin maulidi.
A cewar jami'an 'yan sandan kasar, 'yan bindiga uku ne suka buda wuta kan masu gadin makarantar da horar da harkokin noman, kafin su kutsa cikin dandazon jama'ar. Hukumomin sun kuma yi ikirarin kashe 'yan bindigar wadanda dukkaninsu ke dauke da jigidar bama-bama, tare da kakkabe wajen da lamarin ya faru. Dalibai shida ne dai aka tabbatar da mutuwarsu a harin na wannan Juma'a.