Taliban ta yi tayin sulhu
February 14, 2018Talla
Kungiyar 'yan tawayen Taliban ta kasar Afghanista, ta ce ba zata ki zaman sulhu don kawo karshen yaki ba a kasar, sai dai ta a share guda yi gargadin cewa kalaman nata ba sa nufin alamu ne na gajiyawa ba. Matakan tsananta luguden wuta ta sama da Amirka ke yi kan mayakan Taliban din tun cikin watan Agustan shekarar da ta gabata dai, ya tilasta mayakan bari wasu gundumomi da ma wasu manyan lardunan da suke rike da su a Afghanistan din.
Sai dai mayakan na tawaye na ci gaba da iko da wasu wuraren, inda suke ma maida martani ga zafafan hare-haren da AMirka ke kaddamarwa a kansu, inda ko cikin makonnin da suka gabata sun kaddamar da wasu munanan hare-haren a Kabul da mutane akalla 150 suka halaka.