1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Kasashen Turai sun shirya sake gina kasar

Ramatu Garba Baba
June 25, 2020

A wani taro da aka gudanar a wannan Alhamis, kasashen duniya sun yi alkawarin tallafawa kasar Sudan da sama da dala biliyan daya da miliyan dari takwas don ganin kasar ta farfado da tattalin arzikinta.

https://p.dw.com/p/3eLMz
Sudan Khartum | Proteste & Unruhen
Hoto: picture-alliance/AP Photo

A wani taro da aka gudanar a wannan Alhamis, kasashen duniya sun tashi haikan a kokarin son ganin an sake gina kasar Sudan, sun dai dauki alkawarin tallafawa kasar da alkawuran da suka yi inda tuni aka sami kimanin dala Biliyan daya da miliyan dari takwas a ayyukan na raya kasar da tattalin arzikinta ya rushe a sakamakon rikicin da ya yi awon gaba da mulkin Oumar al-Bashir a bara.

A taron da kasar Jamus ta karbi bakuncinsa, Ministan harkokin wajen Jamus din Heiko Maas, a yayin taron na bidiyo da ya hada da wakilan na Sudan dana Kungiyar tarayyar Turai da kuma na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce taro ne da ya bude sabon babi a sabuwar dangantaka a tsakanin nahiyar Turai da Sudan da ke kokarin sake gina kasa bayan munmunar zanga-zangar neman sauyi.

Jamus ta yi alkawarin zuba Yuro miliyan dari da hamsin yayin da Amurka ta sheda zuba sama da dala miliyan dari uku sai Britaniyya da ta ce za ta bayar da Fam miliyan dari da hamsin da Faransa da ta dauki alkawarin zuba Yuro miliyan dari sai Kungiyar Tarayyar Turai da za ta bayar da Yuro miliyan dari uku da sha biyu, kasashen Chaina da Spaniya kuwa, sun yi alkawarin biyan basusukun da ke kan kasar na sama da Yuro biliyan hamsin da shida. Firaiminsitan Sudan  Abdallah Hamdok, ya yaba da hadin kan da kasar ta samu musanman ta fuskar sake gina kasar.