1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tanka ta kashe rayuka a Tanzaniya

August 10, 2019

Akalla mutane 60 ne rahotanni suka tabbatar da mutuwarsu a Tanzaniya yayin da wasu sama da hakan suka ji jiki, bayan hadarin da wata motar dakon man fetur ta yi.

https://p.dw.com/p/3NhvY
Tansania Morogoro Treibstoff-LKW Explosion
Hoto: picture-alliance/AP

Hadarin ya faru ne a kusa da garin Morogoro da ke yammacin Dar es Salaam babban birnin kasar, a wannan Asabar.

Mutanen da abin ya shafa, galibinsu sun yi kokarin kwashe mai da ke tsiyaya ne daga motar da ta fadin, daga nan kuma ta yi bindiga ta kama da wuta.

Cikin watan Mayun bana, wata tankar ta fadi a kusa da filin jirgi na birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar inda mutane 80 suka mutu.

Ko a bara ma an sami makamanciyar hakan a tsakiyar Najeriya, inda can kuwa sama da mutane 80 su ma da ke kwasar man suka salwanta.