Tanzaniya: Jirgin ruwa ya kife da mutane
September 21, 2018Talla
Tabkin Victoria shi ne tabki mafi girma a nahiyar Afirka, hukumomi sun tabbatar da mutane sama da 100 a cikin jirgin lokcin da ya kife a kusa da tsibirin Ukoro da ke Kudu maso gabashin tabkunan da suka ratsa kasahsen Yuganda da Kenya.
Jami'an agaji sun yi nasarar ceto mutane 37, yayin da ake ci gaba da nemo saura mutanen da suka nitse a cikin ruwa, hukumomi na zargin nauyi sakamakon yawan mutane da buhunan masara da siminti na cikin abin da ya haddasa kifewar jirgin ruwan.