John Magufuli zai sake tsayawa takara
June 17, 2020Talla
Duk da zargin rashin 'yanci da walwala da aka zargi shugaban da aikatawa a wa'adin mulkinsa na farko, Shugaba Magufuli ya sake samun sahalewar jam'iyyarsa ta CCM, wacce ya ce ta zabeshi don ci gaba da aiwatar da ayyukansa na gari a wani sabon wa'adi na biyu na mulki.
'Yan adawa sun sha caccakar gwamnatin John Magufuli, bisa rashin iya jagoranci, sai dai ana hasashen cewa za a gudanar da zaben ne a yayin da kasar ke cikin wani yanayi na fuskantar annobar corona, duk da yake rahotanni na nuni da cewar shugaban na sako-sako da ita.