Tanzaniya: Ministoci su bayyana kadarori ko su bar kujerunsu
February 27, 2016Shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli ya yi barazanar sauke duk wani minista a majalisar zartarwarsa muddin ya ki bayyana kadarorin da ya mallaka. Wannan na zuwa ne cikin fafutikar da sabon shugaban na Tanzaniya ya sanya a gaba ta yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Kasar ta Tanzaniya ta kasance cikin ‘yan gaba-gaba cikin kasashen duniya masu fama da cin hanci da rashawa inda take rike da lamba ta 117 cikin kasashe 168 yayin da kasa mai lamba ta daya ke zama mafi karancin cin hanci a cikin kassahen da rahoton kungiyar Transparency International da ke yaki da cin hanci da rashawa a duniya ta fitar na shekarar 2015.
A cewar jawabin da ya fita daga ofishin Firaministan kasar ta Tanzaniya duk wani ministan da bai bayyana irin kadadrori da ya mallaka ba na da dama ya bayyana zuwa karfe shida na yammacin ranar Asabar din nan.
Hukumar da ke da alhakin tattara wadannan bayanai dai a kasar ta Tanzaniya ta bayyana a farkon makon nan cewa manyan ministoci hudu ne da karamin minista daya ba su bayyana kadarorin nasu ba.