Tanzaniya: Mutane 130 sun halaka
September 21, 2018Talla
Masu aikin ceto sun sa himma a kokari na ganin sun sake zakulo karin na mutanen da ake fargabar sun halaka bayan sun nutse a ruwan tafkin. Jirgin mai suna MV Nyerere na dauke ne da sama da mutane 200 ya kuma kife ne lokacin da yake kusa da tsibirin Ukara kamar yadda kafafan yada labarai a Tanzaniya suka bayyana a ranar Alhamis.
Wadanda suka ga yadda lamarin ya faru sun fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa mutanen da jirgen ya kife da su sun rika rige-rige ne wajen fita lokacin da jirgin ya nufi gabar tafki, lamarin da ya sa ya fi nauyi bangare guda ya kife. Har kawo yanzu dai ana ci gaba da aikin ceton yayin da wasu rahotanni da ke fitowa yanzu ke nuni da cewa an gano gawarwaki 136.